An fadada binciken cin hanci a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Kwamitin da shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya kafa don ya bincika kudaden da ke shiga asusun rara na kasar, ya dauki wasu kamfanoni biyu aiki domin su taya shi aikin bincike.

Kwamitin har wa yau ya ce a yanzu zai fadada bincikensa ya shafi sauran cibiyoyin gwamnatin tarayya da ke samar da kudade, maimakon ya takaita ga kamfanin mai na kasar NNPC.

Gwamnan jihar Edo, wanda shi ne jagoran kwamitin shi ya bayyana hakan bayan taron da suka gudanar jiya a Abuja.

Gwamna Oshiomole ya ce kamfanonin KPMG da kuma PriceWaterHouseCooper ne za su gudanar da binciken a madadin kwamitin binciken.

Sauran hukumomin gwamnati da za a gudanar da bincike a kansu sun hada da hukumar kwastam da kuma FIRS.

Batun cin hanci da rashawa wajen gudanar da ayyukan gwamnati a Nigeria shi ne abin da ake zargin ke janyo tarnaki ga ci gaban kasar.