Mataimakin Gwamnan Borno ya rasu

Hakkin mallakar hoto Borno Govt Facebook
Image caption Labari da dumi-dumi

Gwamnatin Jihar Borno ta sanar da rasuwar Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Zannah Umar Mustapha.

Mataimakin Gwamnan ya rasu ne yau da asuba a Yola, babban birnin jihar Adamawa, inda ya je wakiltar Gwamnan Borno a wajen bikin yaye daliban jami'ar fasaha ta Modibbo Adama.

Wata sanarwar da ta fito daga fadar gwamnatin ta ce za a jana'izar marigayin idan an jima da maraice, a fadar gwamnatin da ke Maiduguri.

Tuni dai gwamnan jihar Bornon, Alhaji Kashim Shettima ya bayyana alhini dangane da wannan rashi, yana adu`ar Allah ya gafarta masa.