Adadin wadanda suka mutu a China ya karu zuwa 85

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wurin da abubuwa suka fashe a China

Adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wasu abubuwa a kusa da wasu masana'antu da ke tashar jirgin ruwa a garin Tianjin na kasar China a ranar laraba ya karu zuwa 85.

Fiye da mutane 700 ne suka samu raunuka a fashewar abubuwan.

A ranar Jumma'a mahukunta a Chinan suka bayar da umarnin da a gudanar da bincike a fadin kasar a wuraren da ake ajiye kayayyaki domin gano ko akwai wasu sinadarai masu guba da kuma abubuwan fashewa.

An dai tura wata tawaga data kunshi mutane fiye da 200 wadanda kwararru ne akan sinadarai domin su je su bawa jami'an kashe gobara shawara akan yadda za a kashe wutar.

Gine-gine sun rushe yayinda motoci da dama suka kone sakamakon fashewar abubuwan.