An tone kajin da hukumar Custom ta binne

Hakkin mallakar hoto MEHR
Image caption Mutanen dai sun tone kajin ne bayan an binne su

Rundunar 'yansanda a jihar kaduna ta cafke mutane sama da talatin wadanda ake zargin su da tono kajin da hukumar hana fasakwauri wato Kwastan ta kona ta kuma binne a kaduna.

Rundunar dai na zargin su ne da bin daji da kuma tono wadannan kaji da naman talo-talo kimanin katon dubu shida da hukumar kwastan din ta kwace wadanda aka hana shiga da su kasar.

Kamar masu hakar zinare dai, wadannan mutane maza da mata sun mamayi wannan daji suka kuma shiga hidimar tono kajin don su ci ko su sayar.

Sai dai kuma jami'an hukumar ta Custom sun ce kajin suna dauke da wani sinadari mai sanya kamuwa da cutar daji.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai hukmar hana fasakwaurin ta kama wadannan kaji da talo-talo wadanda masu su suka yi kokarin shigo da su Njeriyar.

Shigo da irin wadannan abubuwa haramun ne a Najeriya.