An kai hari kauyen Rimirgo a Askira Uba

Dakarun sojin Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin ya zo ne kwana guda da ziyarar da mai ba shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya kai jihar Borno.

Rahotanni daga kauyen Rimirgo da ke Askira Uba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria na cewa wani dan harin kunar bakin wake ya tashe bam din da ke daure a jikinsa a wurin binciken ababen hawa na hadin gwiwa tsakanin 'yan Kato da gora da jami'an tsaro da ke farkon shiga kauyen.

Babu wanda ya rasa ransa a harin baya ga dan kunar bakin wake, amma wani dan kato da gora da wasu mutane biyu sun ji rauni.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da mai ba shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya jagoranci manyan hasan Sojin kasar zuwa jihar Borno, a wani mataki na daukar sabon salo a yakin da ake yi da masu tada kayar baya na kungiyar Boko Haram.

Harwayau ziyarar na nuni da cika umarnin da shugaba Muhammadu buhari ya ba rundunar sojin kasar da su kawo karhen Tada kayar bayan Boko Haram cikin watanni uku masu zuwa.