An hana hawa babura a jihar Adamawa

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jihar Adamawa na fama da hare haren Boko Haram.

Hukumomi tsaro a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Nigeria sun hana hawa babura a duk fadin jihar tun daga karshen wannan makon.

Hukumomin dai na zargin cewa ana amfani da babura ne wajen kai hare-hare da kan yi sanadiyar asarar rayuka.

Jihar ta Adamawa na daga cikin jihohin Nigeria dake fama da hare haren mayakan kungiyar Boko Haram.

Ko a ranar 29 ga watan Okotoba shekarar data gabata, 'yan kungiyar Boko Haram sun kame garin Mubi na jihar Adamawa, har ma suka kafa tutarsu a garin, sai dai daga bisani jami'an sojin Nigeria sun yi nasarar fatattakar su daga garin.