Tsugune bata kare ba a kasar Burundi

Shugaba Pierre Nkurunziza Hakkin mallakar hoto
Image caption Tarayyar Afurka ta yi gargadin barkewar yaki a kasar Burundi idan bangarorin da ke hamayya da juna ba su sasanta ba.

Hukumar Tarayyar Afurka tace kasar Burundi na cike da hadarin barkewar sabon yaki, idan har aka ci gaba da fuskantar rashin zaman lafiya a kasar.

Shugabar hukumar Tarayyar Afurka Nkosozana Dlamini-Zuma ta yi kira ga dukkan bangarorin biyu da ke hamayya da juna da su zubda makamansu, kwana daya bayan kisan da aka yi wa shugaban rundunar Sojin kasar a Bujumburaa.

A makwannin da suka gabata dai an hallaka jiga-jigan 'yan adawa da dama, da kuma masu kin jinin gwamnatin kasar.

Rikicin Burundi ya ta'azzara ne tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta yin tazarce a karo na uku, lamarin da 'yan adawa suka ce ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar hawan kawara.

Amma duk da hakan sai da aka gudanar da zaben, inda ya lashe kuri'u da gagarumin rinjaye.

Duk da kiraye-kirayen da kasashe irinsu Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka yi na a dakatar da yin zaben.