Ana ci gaba da aikin ceto a China

Gobara a kasar China Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kawo yanzu mutane 112 ne suka rasa rayukansu a kasar China.

Kwanaki hudu bayan fashewar wasu abubuwa a kusa da wasu masana'antu da ke tashar jirgin ruwa a garin Tianjin na kasar China, hukumomi sun ce har yanzu akwai kimanin mutane casa'in da biyar da suka bace yawancinsu masu aikin kashe gobara.

Iyalan wadanda ba a gani ba su na gudanar da zanga-zanga saboda babu wani karin bayani da akai musu game da makomar 'yan uwansu.

Sun kuma yi korafin cewa ta yiwu jami'an kashe gobarar ba a basu horo kan yadda za su tunkare kashe gobarar da sinadarai da ababen fashewa suka haddasa ba.

Adadin wadanda suka rasa rayukansu ya karu da mutane dari da goma sha biyu, wani bababn jami'in gwamnatin kasar Sin ya bayyana cewa an fara amfani da jiragen sama marasa matuka da kuma jirage masu saukar ungulu domin duba saman kwanyayin da kuma adadin mutanen da suka mutu ya karu zuwa fiye da mutum dari da goma.

Fiye da mutane 700 ne kuma aka bayyana cewa sun samu raunuka, yayin da wasu da dama ke cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai.

A halin da ake ciki, hukumar dake kula da hanyoyin sadarwar Internet ta rufe ko kuma ta dakatar da wasu shafukan Internet bisa zargin jefa fargaba a zukatan jama'a na wallafa wasu bayanai wadanda ba'a tantance su ba.