'ba mu damu ba ko Shekau na raye ko ya mutu'

Rundunar sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto
Image caption Rundunar sojin Najeriya ta nada sabon kwamandan da zai jagoranci yaki da ta'addanci.

Rundunar sojin Nigeria ta maida martani akan faifai da ke ikirarin cewa jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yana raye bai mutu ba.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria, Kanar Usman Kukah Sheka ya ce rundunar sojin ba ta damu ba akan ko Abubakar Shekau yana da rai ko ba shi da rai.

Ya kara da cewa babban abin da suka sa a gaba a halin yanzu shi ne na ganin sun murkushe kungiyar Boko Haram nan da watanni uku.

Rundunar sojin Najeriyar ta kuma sanar da nadin Manjo Janar Yusha'u Mahmood Abubakar a matsayin sabon kwamandan da zai jagoranci dakarun sojin kasar a yakin da suke yi da ta'addanci.