Abuja: Matasa na jerin gwano zuwa Aso Villa

protest
Image caption Kungiyar na goyon bayan hukunta duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa a kasar ba sani ba sabo.

A yau Litinin ne wasu tarin matasa maza da mata ke jerin gwano zuwa fadar shugaban Najeriya watau Aso Villa.

Za su yi hakan ne domin jan hankalin Shugaban kasar Muhammadu Buhari da kada ya ja da baya game da batun damar da ya daura na yaki da cin hanci da rashawa a kasar

'Yan kungiyar dai sun yi zargin cewa sun sami labari cewa akwai wadanda suke matsin lamba ga Shugaban kasar na ya janye maganar tuhumar mutanen da ake zargin sun wawure dukiyar kasa.

Jerin gwanon ya biyo bayan wata ziyarar da wasu manyan shugabannin kasar suka kai wa Shugaba Buharin, inda suka bukace shi da ya mayar da hankali ga ayyukan ci gaban kasa, ba wai bincike kan zargin satar da aka yi a karkashin gwamnatin da ta bar mulki ba.