Shekau: Ina nan a raye

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau ya sake bayyana

Wani faifan murya ya bayyana na shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau inda ya ke musanta cewar an maye gurbinsa, kuma ya ce yana nan a raye.

A karon farko kuma Jagoran ya ambaci kansa a matsayin Gwamnan daular musulunci na Afirka ta yamma mai mubaya'a ga kungiyar IS.

Ya kuma kalubalanci Shugaban kasar Chadi da kuma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan umarnin da ya bayar na murkushe su cikin watanni uku.

A baya dai an yi ta rade radin cewar Shekau ya mutu.

A makon da ya gabata ma Shugaban Chadi ya ce an maye gurbinsa.