Salva Kiir zai halarci sulhun Addis Ababa

Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar Hakkin mallakar hoto
Image caption Watanni 20 kenan ana dauki ba dadi tsakanin 'yan tawye da gwamnatin Sudan ta Kudu.

Nan gaba kadan ne ake sa ran shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir zai halacci zaman tattaunawar sulhun da ake yi a Addis Ababa baban birnin kasar habasha, wadda ake saran zxa ta kawo karshen zubda jinin da ake yi tsakanin magoya bayan Mr Kiir da tsohon mataimakinsa kuma Riek Machar.

Mai magana da yawun gwamnatin Sudan ta Kudu Areny Wek shi ya sanar da wanann sauyin tsari, kwana guda da shugaba Kiir ya sanar da cewa ba zai halacci zaman sulhun ba, amma mataimakinsa zai wakilce shi.

south_sudan

kamar yadda Mr Ateny ya sanar tafiyar ta Mr Kiir ta biyo bayan matsin lambar da shugabannin yankin da ke shiga tsakani suka yi, an cewa lallai ne sai halarci wanann zama, mai makon tura wakili.

Masu shiga tsakani dan sasanta rikicin da aka kwashe watanni 20 a na yi tsakanin gwamnatin Sudan ta kudu da 'yan tawaye, sun ba da wa'adin gobe litinin 17 ga watan Agusta da su zubda makamansu tare da rattaba hannu kan dawwamammiyar yarjejeniyar zaman lafiya dan ci gaban kasarsu.