Bikin kakar sabuwar doya na 'yan Ibo

A kowacce shekara 'yan kabilar Ibo daga sassa daba-daban na yankin kudu maso gabashin Nigeria suna gudanar da biki na sabuwar kakar doya.

Ana gudanar da bikin ne a tsakanin watan Yuli zuwa na Agusta a duk shekara.

Abin kunya ne a al'adar Ibo, manomi ya girbe doyarsa ko ya ci, ko ya sayar a kasuwa kafin gudanar da wannan bikin na sabuwar kakar doya.

Wakilinmu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya halarci bikin na wannan shekarar da aka gudanar a karshen mako a masarautar Adogbalato da ke karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.

Ga wasu daga cikin hotunan da ya dauko mana.