Salva Kiir ya ki sa hannu a yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Kiir da Riek Machar sun dade suna takun saka

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya ki sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya, wadda wa'adinta zai kawo karshe nan da wasu 'yan sa'o'i.

Wani mai shiga tsakani a tattaunawar da ake yi a Habasha, ya ce gwamnatin Sudan ta Kudu ta na ja a kan wasu batutuwa na yarjejeniyar, kuma sai nan da kwanaki 15 za su sa hannu.

Shugaban 'yan tawaye, Riek Machar ya sanya hannu a yarjejeniyar.

An yi wa bangarorin biyu barazanar takunkumi na kasashen waje idan har ba su amince da yarjejeniyar ba zuwa ranar Litinin din nan.

Ministan Biritaniya mai kula da kasashen Afrika wanda ke halartar taron, ya ce lokacin murna bai yi ba tukuna.

Rikicin Sudan ta Kudu ya janyo mutuwar dubun-dubatar mutane a yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.