Sarkin Misau na jihar Bauchi ya rasu

Image caption Masarautar Misau na karkashin jihar Bauchi

Rahotanni da mu ke samu daga jihar Bauchi a Najeriya na cewa Allah Ya yi wa Sarkin Misau, Alhaji Muhammadu Manga na uku rasuwa.

Sarkin, wanda ya kwashe fiye da shekaru talatin a karagar mulki, ya rasu ne a ranar Litinin bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Za mu kawo muku karin bayani nan gaba kadan bayan an yi jana'izarsa.

Masarautar Misau tana daya daga cikin masarautu masu rike da sarauta mai daraja ta farko a jihar Bauchi.