Za a gurfanar da 'yan BH gaban kotu a Cadi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar 15 ga watan Yuni ne 'yan Boko Haram suka kai hari wani ofishin 'yan sanda a Cadi

Za a gurfanar da wadansu mutane goma wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne a gaban kotu a N'Djamena, babban birnin Cadi.

Kamfanin dillanci labarai na AFP ya ruwaito cewar, ana zargin mutanen ne da shirya hare-haren bama-baman da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 38 a kasar ta Cadi.

A ranar Litinin ne aka mayar da shari'ar kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta Cadi, amma har yanzu ba a sanya ranar fara sauraron karar ba.

Wannan shari'a ta masu tayar da kayar baya masu cibiya a Najeriya, ita ce irin ta ta farko da za a gudanar a kasar Cadi.

A cewar mahukuntan kasar ta Cadi, a cikin wadanda ake tuhumar akwai Mahamat Mustapha, wanda aka fi sani da Bana Fanaye, mutumin da ake zargi da hannu wajen kitsa harin, wanda aka kai a kan wata makaranta da kuma ofishin 'yan sanda a N'Djamena ranar 15 ga watan Yuni.

Kazalika, ana tuhumar Bana Fanaye da samar da makamai da kuma shigar da mutane cikin kungiyar ta Boko Haram.

Cadi dai tana fama da hare-haren kungiyar Boko Haram, kuma tana cikin kasashen da suke yakar kungiyar.