Shugaban Gabon zai raba gadon mahaifinsa

Image caption Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo

Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo Ondimba, ya ce zai rabawa matasan kasar gadon da ya gada daga mahaifinsa -- wanda ya yi shugabancin kasar fiye da shekaru 40.

Ya kuma ce za a bai wa gwamnatin kasar kadarorin da suka zama mallakin mahaifinsa Omar Bongo, wadanda biyu suke a birnin Paris daya a Gabon.

Dukiyar da Mista Bongo ya bari dai ta kai miliyoyin daloli.

Masu shari'a dai a Faransa suna bincike kan kadarorin da shugabannin Afrika suke saya a kasar, wanda ya hada da na Mista Bongo.

Wata kungiyar yaki da karbar hanci da rashawa ta ce da dukiyoyin gwamnati aka sayi irin wadannan manyan kadarorin.