Ghana za ta dauko likitoci 170 daga Cuba

Image caption Marasa lafiya a Ghana suna cikin yanayi mara dadi

Gwamnatin Ghana na shirin shigo da likitoci fiye da 170 daga kasar Cuba domin su yi aiki a asibitocin da likitocin kasar ke yajin aiki.

Ministan lafiya na kasar, Alex Segbefia wanda ya bayyana haka, ya kara da cewa gwamnatin kuma za ta ci gaba da aiki tare da likitocin kasar Cuba wadanda kwantaraginsu ya kare.

Likitoci a kasar Ghana sun soma yajin aiki ne tun a farkon wannan watan saboda su matsa lamba ga gwamnati ta gyara musu yanayin aiki.

An kasa samun maslaha a tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar likitocin.

A halin yanzu asibitocin 'yan sanda da kuma na sojoji sun cika saboda fararen hula da suka je neman magani.