Google ya samar da waya mai sauki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Google ta samar da wayar tafi da gidanka mai saukin kudi ga Afrika

Kamfanin Google ya samar da wayar komai da ruwanka mai saukin kudi ga wasu kasashen Afrika guda shida inda da yawan mutane basa iyabsayen waya mai amfani da intanet.

A ranar Talata ne aka bayar da sanarwar cewa wayar wacce kamfanin Infinix suka yi za a sayar da ita a kan kudi dala 87.

Za a iya samunta a kantuna a Najeriya da kuma kantin sayar da kayayyaki a intanet na Jumia a sauran kasashe biyar da suka hada da Masar da Ghana da Ivory Coast da Kenya da kuma Moroko.

A bara ne kamfanin Infinix ya hada gwiwa da Google wajen kirkiro da manhajar "Hot 2" a wayoyin komai da ruwanka a kasar Indiya.goo