Nakasassun yara ba sa samun gurbin karatu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nakasassun yara na fuskantar kalubale

Wata kungiyar farar hula ta duniya mai sa ido a kan al'amuran da suke tafiya ta ce rabin nakasassun yara basa zuwa makaranta a Afrika ta kudu.

A wani rahoto da hukumar kare hakkin bil'adama ta duniya ta fitar, ta ce da yawa daga cikin yaran sai sun yi jira na tsawon shekaru hudu kafin su samu gurbi a makarantu na musamman da aka yi saboda da su.

Rahoton ya kuma gano cewa sauran makarantu kuma ba sa yarda su bai wa nakasassun yara gurbin karatu, duk da cewar kuwa ya kamata su yi hakan.

Yawancin wadanda aka bai wa gurbin karatu kuwa a sauran makarantu kan fuskanci kalubbale na cin zarafi.

I zuwa yanzu dai, hukumomin Afrika ta kudu ba su mai da martani ba game da zargin da wannan rahoto yake mu su.