Musulmai sun fitar da matsaya kan sauyin yanayi

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption An yi kira da a gaggauta cimma yarjejeniya kan sauyin yanayi

Shugabannin addinin musulunci da manyan malamai daga kasashe kimanin 20, sun yi kira ga gwamnatoci da su zage dantse domin a cimma yarjejeniya sauyin yanayi mai dorewa.

Sun nemi a cimma yarjejeniyar ce a lokacin babban taron kolin da za'a yi kan sauyin yanayi a birnin Paris a watan Disamba.

A wani taro da suka gudanar a birnin Santanbul na kasar Turkiyya, mahalarta taron koli na kasa da kasa na Islama kan sauyin yanayin, sun gabatar da hanyoyin takaita matsalar dumamar yanayi a bisa koyarwar addinin musulunci.

Sun kuma yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arzikin mai da masana'antu da su rage fitar da gurabataciyar isakar gas nan da shekara ta 2050.

Mahalarta taron sun kuma bukaci sauran kasashen duniya ma su mai da hankulansu wajen amfani da sabuwar hanyar amfani da makamashi.