An gano ma'aikatan boge a Kano

Image caption Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano ma'aikatan boge kusan 1,000 daga cikin ma'aikatan shara sama da 2,000 da aka dakatar a farkon watan nan.

Gwamnatin ta ce binciken ta na farko farko ya gano cewa akwai wasu manyan jami'an gwamnati da ke hada baki da wasu don karbar kudi da sunan wasu ma'aikata.

Amma wasu daga cikin masu sharar da aka dakatar na cewa suna cikin mawuyacin halin rayuwa, yayin da gwamnatin ta Kano ke ci gaba da shan suka kan matakin dakatar da masu sharar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Comrade Muhammad Garba, ya ce "Idan har an kammala bincike gwamnati za ta dauki tsattsauran mataki ta kuma tabbatar da hukuncin da ya dace ba tare da la'akari siyasa ba."