Togo ta damu kan tura yara aikatau

Hakkin mallakar hoto Public Domain
Image caption Tutar Togo

Togo na fama da matsalar tura yara mata da maza aikatau a gonaki da kuma gidaje a Lome da kuma safarar su zuwa makwabta Najeriya da Benin.

Ana zargin karancin ilimi da fatara da kuma rashin harkar kasuwanci a tsakanin magindanta shi ne ya ta'azzara bautar da yaran da kuma fataucinsu daga kauyuka zuwa birane a ciki da kuma wajen kasar.

A wani kauye da ke kan iyakar kasar da Benin da kuma Najeriya, an yi safarar dubban yara mata domin su yi aikatau, a inda iyayen gidajensu ke musguna musu gami da cin zarafin su baya ga hanasu zuwa makaranta.

Masu safarar na karbar alabashin yaran na wata uku ko hudu a mtasayin kafin alkalami a inda za su yi aiki, sai su ba iyayen yaran wani kaso, bayan watannin bakwai ko takwas kuma sai su dawo da yaran kuyukansu.

Kungiyoyin sa kai na taimakawa yaran da suka gudo ta hanyar sa su a makaranta da koya musu sana'a, tare da jan hankalin masu safarar yaran da su daina ta hanyar nuna musu illar abinda suke yi.

Bincke ya gano cewa masu safarar na yi ne domin samun abinda za su ci.