Ko wasan kwamfuta na harzuka mutane?

Wasan vidiyo kwamfuta Hakkin mallakar hoto TWITCH
Image caption Masana sun ce akwai rauni a hanyoyin da aka bi wajen gudanar binciken

Fiye da malamai dari biyu sun sa hannu a wata budaddiyar wasika inda suke sukar wani bincike mai cike da cece kuce daya nuna alaka tsakanin wadanda ke kallon wasan kwamfuta da kasancewa masu zafin rai.

Wata kungiya ta masana kan halayyar dan Adam ta Amurka ce ta fitar da sakamakon binciken.

Kungiyar ta yi nazari akan daruruwan binciken da aka gudanar da kuma takardu da aka buga tsakanin shekarun 2005 da 2013.

Sakamakon binciken ya nuna cewa ana samun dangantaka tsakanin kallon wasannin vidiyo na kwamfuta da kuma karuwar masu zafin rai.

Sai dai wasu masana sun ce akwai rauni matuka a hanyoyin da aka bi wajen gudanar binciken saboda gazawar da aka yi na gabatar da sakamakon binciken don karin nazari mai zurfi.