EU ta bukaci a magance matsalar bakin haure

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Turai na fama da matsalar tururuwar bakin haure

Hukumar da ke kula da kan iyakoki ta kungiyar Tarayya Turai, Frontex, ta bukaci kasashen kungiyar da su taimaka wa kasashe uku na kungiyar wadanda suka fi fuskantar matsalar tururuwar bakin haure.

Kashashen dai su ne Girka da Italiya da kuma Hungary.

Hukumar ta bayyana yawan bakin hauren da kan kwarara zuwa nahiyar Turai a matsayin wani al'amari da ke bukatar kulawa ta gaggawa.

Haka kuma hukumar ta Frontex ta bukaci karin ma'aikata da kayan aiki tana mai cewa a watan da ya gabata, bakin haure fiye da 100,007 ne suka shiga nahiyar Turai ta barauniyar hanya, wanda ya nunka adadin wadanda suka isa a watan Yuli har sau uku.

Wani wakilin BBC ya ce galibin bakin hauren da kan shiga Turai sun fito ne daga kasashen Syria da Afghanistan wadanda ke shiga kasar Girka ta Turkiya, yayin da wadansu kuma 'yan Afrika ne da suka fito daga Najeriya da Eritrea wadanda kan tsallaka ta Libiya zuwa kasar Italiya.