Mai digirin-digirgir ya buge da kwashe bola a Indiya

Image caption Duk da kwalin digiri hudu da Mista Sunil ya mallaka, sai gashi ya bige da kwasar bola

Sunil Yadav, mai shekaru 36 dan asalin birnin Mumbai ne na kasar Indiya, kuma mutum ne da ya yi amanna kwarai da karatun boko.

Yana da kwalin digiri hudu wanda ya hada da digirin-digirgir da ya samu daga kwalejin Tata, yanzu haka kuma yana kokarin kammala wani digirin-digirgir din nasa.

Kazalika, katin shaidar wajen aikinsa na nuna cewa har yanzu aikinsa shi ne kwasar bolar da kwasar kashi.

Mista Yadav ya ce wani mai fafutika kare hakkin dan adan R Ambedkar, ne ya ankarar da shi muhimmancin ilimi tare da nuna masa cewa ilimi shi ne jigon rayuwar dan adam da zai iya samar masa kowanne irin canji.

Amma ga dukkan alamu shi bai samu irin canjin da yake bukata ba.

'Ilimi gishirin zaman duniya'

Image caption Mista Yadav ya gaji mahaifinsa ne

Duk da kwalayen digirin da Mista Yadav ya mallaka hakan bai sa ya samu karin girma a wajen aikinsa ba, wanda yake yi karkashin hukumar birnin Mumbai da kewaye.

A yanzu haka dai aikinsa shi ne, bi lungu-lungu na birnin Mumbai da daddare domin kwashe shara, da rana kuwa ya kan mayar da hankali ne wajen karatunsa a makaranta.

A kan bai wa dukkan ma'aikata damar su tafi karo karatu kuma su ci gaba da aiki amma Mista Yadav ya ce an ki a yarda da bukatarsa kan hakan duk da cewa a baya-bayan nan ma ya nemi alfarmar hakan.

Mista Yadav ya ce "Daya daga cikin jami'an wajen ya shaida mini cewa idan har ya bani dama to hakan na nufin sai ya bai wa kowa dama. Ya ce mini wai me zan samu ne a karatun da na damu kaina da yi? Gaskiya hukumar wajen aikin ta mayar da mu tamkar bayi."

A lokacin da ya yi digirin-digirgir dinsa na biyu ma sai da ya yi bore na 'yan watanni sannan aka bashi hutun karatu.

Karamar hukumar Mumbai da kewaye, ita ce karamar hukuma ma fi yawan arziki a Indiya.

Tana da kimanin ma'aikata masu tsaftace muhalli kimanin 28,000 da kuma leburori 15,000.