Ana samun karuwar fyade a Sokoto

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An soma shari'ar wasu da ake zargi da fyade a Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto da ke arewacin Nigeria, sun yi gargadin cewa ana samun karuwar aikata yi wa mata da 'yan mata fyade a jihar.

Gargadin na zuwa ne bayan da wasu matasa suka yi wa wata yarinya 'yar shekaru 14 fyade tun cikin dare har zuwa wayewar gari a cikin wani gida a garin Sokoto.

Tuni aka tsare matasa biyu bisa zargin aikata fyaden a yayin da matashin na uku ya gudu ake nemansa ruwa a jallo.

Ofishin kare hakkin bil adama na gwamnati a jihar Sokoto, ya ce cikin watanni shida da suka wuce an kai musu kara kan zargin fyade har guda 28.

Batun yi wa mata fyade a Nigeria wani lamari ne mai sarkakiya saboda wasu iyayen ba sa son su kai kara idan an yi wa 'ya'yansu fyade saboda gudun ka da a nuna musu wariya a al'umma.