Kauyukan Zamfara sun koka da rashin hanya

Image caption Rashin kyawun hanya na addabar mutanen karkara

Wadansu 'yan asalin jihar Zamfara mazauna jihar Kaduna a Najeriya, sun koka da rashin kyawun hanyoyi a wasu sassan, musamman a yankunan karkara na kudancin jahar, inda suke zargin gwamnati da rashin mayar da hankali a kansu.

'Yan jihar ta Zamfara sun kuma ce rakuma da jakuna suke hawa domin zuwa kasuwa sanadiyyar rashin hanyoyi a yankin Mada da kewaye.

Sai dai gwamnatin jihar ta musanta zargin.

Kakakin mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Yusuf Idris Gusau, ya ce, "Wannan dai suna fadin son ransu ne kawai amma akwai hanyoyi masu kyau da za su sada mutum da kauyen Mada, wanda gwamnatin baya-bayan nan ma ta yi."

Rashin kyawun hanyoyi na cikin matsalolin da ke addabar mutanen karkara, lamarin da ke sa mazauna yankunan su dinga muradin yin kaura zuwa birane domin samun abubuwan more rayuwa.