Zan dawo Kannywood - Abba Ruba

Image caption Abba ruba ya dauki hutu ga harkar fina-finan Hausa domin neman karin ilimi da kuma shiga siyasa.

Abba Al-Mustapha wani tauraren fina-finan Hausa, ya shaida wa BBC cewar ya kwana biyu baya sana'ar ta fim ne, domin ya je neman karin ilimi da kuma neman shiga siyasa, inda bai yi nasarar cimma burin sa ba.

A hirarsa da BBC, Abba Al-Mustapaha wanda ake kira 'Abba Ruba' ya ce nan ba da jimawa ba zai kara komawa shiga cikin fina-finan Kannywood bayan hutun da ya dauka na wani dan lokaci.

"Na ga ne a shekaru na akwai burin da nake so na cimma, na farko shi ne ina son in kara zurfafa ilimi na, na biyu kuma ina so in shigo in bayar da gudunmuwa ta a bangaren siyasa,"In ji Abba Al-Mustapha.

Ya kara da cewar "A lokacin da aka ji ni shiru, na canza tsarin rayuwata ne inda na koma makaranta."

Fina-finan Hausa da ake kira Kannywood na cikin rukunin adabi da Hausawa da ke da farin jini tsakanin matasa maza da mata.

Wasu masu sharhi na ganin a maimakon fina-finan su gyara tarbiyya da kuma aikewa da sakonni na gari, masu yin fina-finan na taka rawa wajen bata al'adun bahaushe, ko da yake masu shirya fina-finan sun sha musanta wannan zargi.

Haka kuma, ana ganin rashin fadin ilimi da kuma mai da hankali wajen samun riba ne ke hana shirya fina-finai masu inganci.