Ana kutse a shafin Ashley Madison

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu kutse a komputa

Da alamu masu kutse a shafukan Komputa sun saki bayanai da yawansu ya kai gigabytes 10 da suka sato daga wani shafin sada zumunta na ma'aurata wato Ashley Madison.

Masu kutsen sun ce sun watsa bayanan na shafukan ma'aurata miliyan 33, wadanda yanzu masu bincike akan harkokin tsaro ke nazari akai.

Yawancin kwararru a bangaren tsaro ciki har da Brian Krebs sun yi amanna cewa bayanan na gaskiya ne.

Sai dai kuma, ba lallai bane dan kana da adireshin email da ke da alaka da wani adireshin ya zama cewa kana amfani da shafin Ashley Madison ba.

Masu amfani da shafukan intanet zasu iya amfani da shafin na Ashley Madison ba tare da sun bi dokar tantance adireshin su na email ba.

Hakan dai na nufin za a iya kulla alaka da kowanne adireshi na email, saboda ba a bin diddigi.

To sai dai duk da wannan ikirari na masu kutsen, wani labari mai dadi ga masu amfani da shafin Ashley Madison shi ne lambobin sirrin su na shiga shafin har yanzu suna nan akan tsarin da ake dashi na yadda za ayi wahalar gane su.

Dangane da haka, ana ganin cewa abune da ya dace ga masu amfani da shafin Ashley Madison su canza lambobin su na sirri wato na bude shafin a wasu shafukan na daban.