Karancin kayan masarufi na shafar Bangui

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahamat Kamoun, Firayi Ministan Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Karancin kayan masarufi ya fara shafar Bangui, Babban birnin Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Wannan ya biyo bayan yajin aikin da direbobin manyan motoci masu dakon kaya a Kamaru suke yi a farkon makon nan, sakamakon rashin tsaron da suke fuskanta daga wasu kungiyoyi masu rike da makamai.

Hakan ya sa a yanzu matuka motocin jamhuriyar tsakiyar Afrika ne kawai suke yin balaguro tsakanin biranen Douala da Bangui tare da rakiyar jami'an tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

A yanzu haka ana kiyasta cewa motoci sama da 100 ne suka yi jerin gwano a tsakanin iyakokin Kamaru da jamhuriyar tsakiyar Afrika ta garin Garwa Bulai.

Direbobin sun tsayar da motocin ne saboda su nuna fushinsu game da kisan rayuka da ake ta yi musu a lokuta da dama idan sun shiga Jamhuriyyar tsakiyar Afrika.

Sun kuma nemi gwamnatocin kasashen biyu su magance matsalar, tare da cewa idan har ba a shawo kan wannan kisan da ake musu na ba gaira ba dalili ba, za su ci gaba da yajin aikin har zuwa lokaci da basu ambata ba.

Farashin kayan abinci da kuma na gini sun karu da kusan kashi 15 zuwa 20 sakamamakon wannan yajin aiki.