An kama 'yan Boko Haram a Maiduguri

Image caption Yanzu haka an damka 'yan Boko Haram din a hannun sojoji

Bayanai daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewacin Najeriya na cewa 'yan sintiri da aka fi sani da civilian JTF sun cafke wasu mutane guda hudu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne.

Wata majiya da ba ta son a bayyana sunanta ko muryarta ta shaida wa BBC cewa da yammacin ranar Laraba ne 'yan sintirin suka kama mutanen hudu a kan hanyarsu ta shiga Maiduguri daga garin Dikwa.

Ana tsammanin cewa luguden wutar da sojojin Najeriya ke yi wa 'yan kungiyar ne yasa su neman barin maboyarsu.

Kawo yanzu dai majiyar ta ce 'yan sintirin sun mika wa rundunar soji ta sector 2 da ke Maidugurin wadanda ake zargin.