Dole a bi tsari wajen daukar 'yan sanda — Buhari

Hakkin mallakar hoto
Image caption Buhari ya ce ba zai lamunci cuwa-cuwa ba

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya umurci sufeto janar na 'yan sandan kasar da ya kula da cewa ba a karbi kudade daga hannun mutane ba a lokacin daukar aikin dansandan da gwamnatin tarayya ta ce za ta yi har mutum dubu 10.

A tattaunawarsa da jami'an ma'aikatar kula da harkokin 'yan sanda, shugaba Buhari ya ce lokacin yin hakan ya wuce.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, ta ce shugaba Buhari ya yi gargadin cewa ba zai yarda da duk wani nau'i na cuwa-cuwa ba wajen daukar 'yan sanda aiki a kasar.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption An zura ido a gani ko shugaban 'yan sanda Arase zai aiwatar da umurnin

Buhari ya ce abin kunya ne a ce mutum sai ya biya kudi sannan a dauke shi a aikin dan sanda, kuma ba zai lamunci hakan ba.

"Dole ne a tabbatar da cewa an yi gaskiya wajen daukar 'yan sanda ba tare da karbar na goro ba," in ji Buhari.

Harwayau, Buharin ya ba da umarnin rage yawan 'yan sandan da ake ba wa manyan mutane, a inda ya ce a maimakon hakan kamata ya yi a tura 'yan sandan zuwa ayyukan tsaro gadan-gadan.

A jawabinsa, shugaban hukumar kula da al'amuran 'yan sanda a Nigeria, Mike Okiro ya ce akwai bukatar a samar da 'yan sanda fiye da wadanda ake da su a yanzu.

A yanzu haka dai Nigeria na da 'yan sanda 305,579.