Shugaba Nkurunziza ya sha rantsuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan adawa sun ce tazarcen Nkurunziza ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

An rantsar da Pierre Nkurunziza a matsayin shugaban kasar Burundi karo na biyar a wani biki da aka gudanar a ranar Alhamis.

Ba a sanar da bikin rantsar da shugaban ba, sai jim kadan kafin a yi rantsuwar.

A watan da ya gabata ne aka gudanar da zaben kasar wanda 'yan adawa suka kaurace masa tare da gudanar da zanga-zangar kin goyon bayan tazarcen shugaba Nkurunziza.

'Yan adawa sun ce tazarcen na sa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Babu wani shugaban wata kasa da ya halarci bikin rantsuwar Mista Nkurunziza.

Amma gwamnatin Burundi ta ce kasashe da yawa sun bayar da hakurin rashin tura wakilansu saboda daga ranar da aka yi.