Intel: Fahimtar maganar masu larurar kwakwalwa da kwamfuta.

Image caption Farfesa Howkings ya dade yana amfani da komfuta wajen sadarwa

Kamfanin Intel wanda ya kirkiro wata fasaha da take taimaka wa farfesa Stephen Hawking, wani dan Birtaniya mai fama da larurar kwakwalwa da laka, ya yi magana ta kwamputa, ya saki fasahar akan intanet.

Fasahar dai tana sauya alamomi da mutum yake nunawa zuwa rubutattun kalmomi sannan daga bisani komfutar ta karanta kalmomin kuma jama'a su fahimta.

Wannan fasaha tana fahimtar motsin kumatuna da ma sauran gabban farfesa Hawkings, kana kuma ta mayar da su zuwa kalmomi kafin komfuta ta karanta su a magance.

Kamfanin na Intel dai ya fara kirkiro wannan fasahar ce domin amfanin farfesa Hawking kawai duk kuwa da cewa wasu masu fama da irin cutar da farfesa yake fuskanta sun yi amfani da fasahar.

Yanzu haka dai kamfanin y saki fasahar akan intanet domin amfanin mutane kuma duk mai bukata zai kwafo fasahar daga intanet din don yin bincike akai.

Kamfanin ya yi hakan ne bisa fatan cewa manazarta masu kokarin fito da fasaha irin wannan domin taimaka wa masu larurar kwakwalwa, za su yi matashiya akai.

Intel ya dora wannan fasahar ne akan manhajar Windows 7.

Hakkin mallakar hoto intell
Image caption Wasu daban suna amfani da irin wannan fasahar

Kungiyar masu larurar kwakwalwa da laka sun yaba da wannan yunkuri a inda suke cewa hakan zai taimaka wa mutane gaya wajen fahimtar masu irin wannan larurar.