Koriya ta Arewa za ta shiga yaki da Koriya ta Kudu

Shugaba Kim Jong-un na Koriya ta Arewa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba Kim Jong-un na Koriya ta Arewa

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya umarci rundunar sojin kasar da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin shiga yaki yayin da zaman dar-dar tsakanin kasar sa da Koriya ta Kudu ke kara tsananta bayan da aka yi musayar wuta tsakanin kasashen biyu.

Kafafen yada labarai na Korea ta-Arewa sun ce shugaban kasar, Kim Jum-un ya ayyana yiwuwar wani dan kwarkwaryar yaki a wani taron gaggawa da ya yi .

Kuma kasar Korea-ta-Arewar ta ce ba gudu ba ja da baya har sai Korea ta Kudu ta dakatar da kamfe din batanci ga mulkin kwamunisanci da take yi akan iyakar kasashen.

Irin wannan barazanar da Korea ta arewa ke yi dai ba yau ta fara ba domin ta yi irinsu a baya amma kuma ba a iya kai wa ga filin daga .

Wakilin BBC a Korea ta Kudu, Steve Evans ya ce duk da cewa barazana tsakanin kasashen biyu ba ta kai wa ga a gwabza amma wannan karon alamu na nuna cewa kowa ya ja daga kuma an daddasa makamai da sojin yaki a yanayi irin na-kule da chas.