Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana yawan aiwatar da hukuncin kisa a Saudiyya

Kasar Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa a kan wasu maza 'yan kasar Chadi biyu a kan rawar da suka taka a wani mummunan hari da kungiyar Alka'ida ta kai kan 'yan kasashen waje.

An samu mutanan biyu da kisan wani injiniya Ba-faranshe a birnin Jiddah a shekara ta 2004.

Wannan na daya daga cikin kashe kashen 'yan kasashen yammaci da ma jami'an gwamnati da aka yi ta yi na tsawon shekaru uku.

Sama da mutane dubu 11 da ake zargi ne aka kama yayin da dakarun tsaron Saudiyyar ke kokarin kakkabe kungiyar Alka'ida da kuma kawo karshen zubda jini a kasar.