Shin ko kasan illar sauro ga rayuwarka?

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Sauro zai iya kisa ko kuma ya taba kwakwalwar mutum

Ranar 20 ga watan Agustan kowace shekara ce ranar da kasashen duniya suka ware domin yaki da sauro.

An kuma kebe ranar ne da manufar fadakar da al'ummar duniya dangane da illolin da sauron yake haddasawa.

Masana dai sun ce cizon sauro na haddasa matsaloli ga wanda ya ciza da suka hada da raguwar jini da zazzabi mai tsanani da kuma hana cin abinci.

Idan cutar ta yi kamari za ta iya sanya mace mai ciki ta yi bari ko kuma a haifi jariri mai dauke da kwayar cutar Malaria.

Babbar illar ta sauro ita ce taba kwakwalwa da kuma yin sanadin mutuwar mai dauke da cutar.

A rana irin wannan dai ana kuma yin nazari kan irin nasarorin da aka samu wajen yaki da sauron.

Masanan dai sun ce tsaftace muhalli da kwanciya a gidan sauro sannan kuma gwamnatoci su dauki matakan kashe saurayen, su ne hanyoyin da za a iya gudar cutar cizon sauro.