Ban Ki Moon ya gana da Buhari

Image caption Mr Ban ya ajiye furanni domin tunawa da mutanen da aka kashe a harin da Boko Haram ta ka kai a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2011.

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Shugabannin biyu sun tattauna a kan al'amuran da suka shafi yaki da ta'addanci da irin rawar da Najeriya ke takawa a Majalisar Dinkin Duniya.

A jawabinsa, Mr Ban ya ce Majalisar Dinkin Duniya za ta bai wa shugaba Buhari goyon baya a yunkurin da yake yi na kawar da ta'addanci da tabbatar da tsaro, yana mai cewa akwai bukatar hada gwiwa domin magance matsalolin.

Ya kara da cewa yana so Najeriya ta samar da ayyukan yi ga matasa domin rage matsalolin tsaro da ke addabar 'yan kasar, musamman a arewa maso gabashin kasar.

A nasa jawabin, Shugaba Buhari ya godewa Sakataren Majalisar Dinkin duniya a kan kokarinsa wajen ganin an samu zaman lafiya a Najeriya.

Ya kara da cewa za su tattauna sosai da Sakataren a taron da za su yi a Majalisar a watan gobe.

Gabanin ganawar ta su, Mr Ban ya kai ziyara ofishin majalisar ɗinkin duniya da ke Abuja, inda ya ajiye furanni domin tunawa da mutanen da aka kashe sakamakon harin da 'yan Boko Haram suka kai a ofishin a shekarar 2011.

Kazalika ana sa ran Mr Ban zai gana da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam cikinsu har da ƙungiyar da ke fafutikar ganin an ceto 'yan matan Chibok fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace.