Soji sun kama kayan 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin wasu na kai wa 'yan Boko Haram makamai.

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama motocin tirela guda biyu dauke da kayayyakin da za a kai wa 'yan kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da rundunar sojin saman kasar ta fitar ta ce wani jirgi mai saukar ungulu na soji ne ya hango tirelolin a kan iyakar Najeriya da Kamaru, kuma nan take aka kama su.

Sanarwar ba ta bayyana ire-iren kayayyakin da ke cikin motocin ba, sai dai ta ce an lalata su.

Kazalika, rundunar ta ce 'yan ta'addan sun harbi jirginta, amma ba su lalata shi sosai ba.

Da ma dai 'yan Najeriya sun sha zargin wasu da aike wa da 'yan Boko Haram kayayyaki da makamai.