Za a kafa sabuwar jam'iyya a Girka

Image caption 'Yan majalisar Girka

'Yan majalisar Girka 25 na jamiyyar Syriza sun ce za su bar jamiyyar su kafa wata sabuwa, kwana daya bayan firayim ministan kasar, Alexis Tsipras, ya yi Murabus daga mukaminsa.

Tsohon ministan kasar, wanda yake sukar makatan tsuke bakin aljihu da Mr Tsipras ya dauka ne yake jagorantar kungiyar.

Shugaban Girka ya bai wa 'yan hamayya masu ra'ayin rikau kwanaki uku su yi kokari su kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa.

Shugaban 'yan hamayya, Vangelis Meimarakis, ya ce zai yi yunkurin yin hakan domin kauracewa yin zaben wuri.