Isra'ila ta kashe mutane hudu a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

A kalla mutane hudu da ke tafiya a mota ne suka mutu bayan wani hari da rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai a makwabciyar yankin Syria.

Majiyoyi a Syria sun ce wadanda harin ya shafa fararen hula ne.

Sai dai sojin Israi'lan sun ce mutanen 'yan bindiga ne wadanda su ne suka harba makaman roka kan Israi'la a ranar Alhamis da ta gabata.

A cewar sojin, mutanen sun jefo makamai masu linzami hudu kodayake babu wanda ya jikkata sakamakon hakan.

Israi'la ta dora laifin harin a kan masu fafutukar kafa daular musulinci da gwamnatin Syria.

Rundunar sojin Syria ta ce an kashe daya daga cikin sojojin ta a jerin hare haren da Israi'la ta kai a yammacin ranar Alhamis.