Nakiya ta tashi da sojoji biyu a Dikwa

Image caption Sojin biyu sun rasu ne sakamakon taka nakiya da suka yi

Sojojin Najeriya biyu ne suka rasu yayin da wasu biyu kuma suka jikkata sakamakon taka nakiya da suka yi wadda mayakan Boko Haram suka binne, a kan hanyarsu ta shiga garin Dikwa.

A wata sanarwa da kakakinta, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, ya fitar, rundunar sojin kasar ta ce tuni aka kwashe gawarwakin aka kuma kai wadanda suka yi raunin asibiti.

Sojojin Najeriya na ci gaba da kwance nakiyoyin da mayakan Boko Haram suka binne a hanyoyin da ke tsakanin wasu garuruwa na jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta kara da cewa a ranar Juma'a ne Runduna ta Bakwai ta Sojin Kasa ta kutsa garin Gudumbali da ke karamar hukumar Guzamala a jihar ta Borno a ci gaba da yakin da ake yi don murkushe 'yan Boko Haram mai taken "Operation Lafiya Dole."

A yayin da suke kai hare-haren, an kashe mayakan kungiyar da dama tare da lalata makamai, inji sanarwar.

A Litinin din da ta gabata ne dai Rundunar Sojin Sama ta Najeria ta lalata sansanonin mayakan na Boko Haram da dama a yankin.