An tsare 'yan Najeriya bisa alaka da IS a India

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An kama matasan ne a garin Punjab mai iyaka da Pakistan

Rahotanin daga India na cewa jami'an tsaron kasar sun kama wasu matasa biyu dalibai dake karatu a kasar lokacin da ake zargi suna kokarin tsalkawa kasar Pakistan domin shiga kungiyar IS.

An dai ce an kama matasan ne a garin Punjab dauke da takardun tafiye-tafiye na boge kuma an yi zargin cewa sun kudiri aniyar shiga kungiyar masu Jihadi ta IS.

Bayanai sun ce daliban biyu wadanda dukkannin su 'yan asalin jihar Kano ne da ke arewa maso yammacin Najeriya sun samu damar shiga kasar ta India ne da nufin yin karatu a birnin Delhi bayan samun umarnin zaman kasar a 2014.

Yanzu haka dai ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya ta ce ta nemi gwamnatin kasar India akan ta ba su damar ganawa da matasan don tantance ko 'yan Najeriyar ne.

Ita ma gwamnatin jihar Kano ta ce tana gudanar da irin wannan bincike kuma sun gano cewa daliban ba sa jerin daliban da gwamnati ta dauki nauyin karatunsu.