Kasuwar wayar Smartphone ta fadi a China

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kasuwar smartphone din ta fadi wqarwas a China

Kasuwar wayar hannu ta komai-da-ruwanka da aka fi sani da smartphone ta fadi warwas a China.

An gano hakan ne dai sakamakon wasu alkaluma da kamfanin bincike na Gartner ya tattara.

Alkalumman dai sun nuna cewa kaso hudu ne na wayoyin smartphone din suka sami shiga a watannin Aprilu da Mayu da kuma Yuni, idan aka kwatanta da watannin a shekarar 2014.

Binciken ya kara da cewa rashin cinikin ya faru ne saboda yawa da wayar ta yi a kasuwa.

An dai ce kusan rabin mutanen kasar ta China suna da wayar ta smartphone amma kuma ba sa iya sauya wayar a duk shakara.

Sai dai kuma ba smartphone ne kawai ke fuskantar irin wannan rashin kasuwar ba.

Cinikin Samsung ma ya yi kasa da kaso 49 duk kuwa da cewa kamfanin ya fito da sabon samfirin wayar na Galaxy S6 kasuwa.

Amma kasuwar Apple kuwa ta samu tagomashi da kaso 68 duk kuwa da cewa kamfanin bai fito da sabbin samfirin wayoyi ba.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mutane suna mallakar smartphone amma ba sa sabunta ta a duk shekara

Ita kuwa Huawei tana bozo a kasuwar ta China a inda bukatarta ta daga da kaso 46.