An kaddamar da littafi don gudun bata yara

Image caption An kaddamar da littafi don gujewa lalata yara a Uganda

A ranar Juma'a ne aka kaddamar da wani littafi mai suna " Bad Touch", wanda yake magana a kan yadda kananan yara za su kare kansu daga masu son yin lalata da su.

Wata marubuciya 'yar kasar Uganda, Lillian Butele Kelle, ce ta rubuta littafin domin kananan yara, wanda ya kunshi zane-zane da ke nuna wuraren da bai kamata yara su bari wani yana taba musu ba.

Iyaye da dama dai na jin nauyin tattaunawa da 'ya'yansu a kan abin da ya shafi jima'i, har ma wasu na tababar ta ina za su fara.

Wannan dalili ne ya sa yake da wuya su yi musu magana a kan masu bata yara, da yadda za su fahimci hakan har ma su kai rahoto in suka samu kansu a wani hali makamancin haka.

Lalata da kananan yara dai ta zama ruwan dare a tsakanin al'umma ta yadda har a wadansu lokutan a kan samu makunsantan yaran ma na da hannu a irin wannan muguwar dabi'a.