Bam ya tashi a sansanin sojin Somalia

Masu tada kayar baya na Al_Shabab Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Al_Shabab sun dade su na kai hare-hare a kasar ta Somalia

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a kudancin kasar Somalia a wani sansanin horas da sojoji ya hallaka mutane 9.

Wata mota da aka ajiye ta makare da bama-bamai ta tarwatse a birnin Kismayo mai tashar ruwa.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afurka a Somalia, sun ce an hallaka maharan guda biyu.

Ya yin da yawancin dakarun wanzar da zaman lafiyar suka ji munanan raunuka.

Yankin Kismayo dai shi ne wuri na karshe da masu tada kayar baya na kungiyar Al-Shabab ke da karfin iko a kasar ta Somaliya.