An kama matashi da makamai a jirgin kasa

Image caption Mutumin yana dauke da bindigogi da wuka

Fassinjojin wani jirgin kasa a Faransa sun murkushe wani matashi wanda ke dauke da muggan makamai suka kuma kwace su daga hannunsa.

Jirgin dai ya taso ne daga birnin Amsterdam na kasar Netherland zuwa birnin Paris a Faransa.

An dai ce mutumin mai shekaru 26 wanda kuma dan asalin kasar Morocco ne, yana dauke da bindiga kirar machine gun da kuma karamar bindiga gami wuka.

Sai dai kuma mutane uku sun jikkata a kokarin da suke yi na kwace makaman.

Wasu 'yan Amurka guda biyu wadanda ake kyautata zato sojoji ne suka murkushe matashin suka kuma karbe makaman.

Tuni dai 'yan sandan Faransa masu sanya ido kan ta'addanci suka fara bincike kan al'amarin, bayan da suka damke matashin.