Za a sasanta Koriya ta Kudu da ta arewa

Shugaban Korea ta arewa
Image caption Korea ta arewa ta dade ta na gargadin Korea ta kudu, kan abinda ta kira tsokanar fada.

Manyan jami'ai na kasashen Koriya ta arewa da Koriya ta kudu suna gudanar da wata tattaunawa a kokarin kwantar da hankula akan iyakokinsu.

Taron na gudana ne a yankin da aka haramta ayyukan soji tsakanin kasashen biyu.

Manyan na hannun daman shugabannin sun gaisa da juna tare da murmushi sabanin irin kurarin da suka rika yiwa juna a baya.

Bangarorin biyu sun amince su tattauna ne jim kadan kafin cikar wa'adin da Koriya ta arewa ta baiwa Koriya ta kudu ta dakatar da yada farfagandar kin jinin kwamunisanci akan iyakar.

Sai dai mataimakin jakadan Koriya ta arewa a Majalisar Dinkin Duniya An Myong-Hun yace sojojin Pyonyang za su bude wuta idan Seoul ta ki bada hadin kai.