Ban Ki-Moon ya soma ziyara a Najeriya

Ban Ki-Moon Hakkin mallakar hoto

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya kammala wata ganawa da galibin gwamnoni jihohin Najeriya 36 a farkon wata ziyarar wuni biyu da ya kai kasar.

Cikin batutuwan da suka tattauna da gwamnonin har da batun yadda za a cim ma muradun cigaba mai dorewa, musamman da yake suna kusa ga jama'a fiye da gwamnatin tarayya.

A gobe ne dai ake sa ran ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari bayan aza furanni a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja domin tunawa da wadanda suka mutu cikin wani harin bam da Boko Haram ta yi ikirarin kaiwa shekaru hudu da suka wuce.